​Kamaru: An Zargi ‘Yan Aware Da Sace Mutane Da Dama

2020-02-13 19:13:02

An zargi kungiyar ‘yan a waren kasar Kamaru da ke dauke da makamai da sace mutane fiye da 100, kafin gudanar da zabukan ‘yan majalisa a karshen makon da ya gabata.

A cikin wani bayani da kungiyar kare hakkin Dan adam ta Human Rights watch ta fitar ta bayya cewa; mayakan 'yan awaren Kamaru sun sace mutane sama da 100 da kuma kona tarin kaddarori kafin zaben na karshen makon jiya.

Daraktan kungiyar da ke kula da tsakiyar Afirka, Lewis Mudge ya ce ya zama wajibi shugabannin 'yan awaren su bayyana wa magoya bayan su cewar su daina kai hare hare kan fararen hula.

Kungiyar ta ce baya ga sace mutane, mayakan ‘yan arewa sun kona kaddarori masu tarin yawa na jama’a, wanda hakan babban laifi ne bisa dokokin duniya.

Haka nan kuma a daya bangaren kungiyar ta Human Right Watch ta zargi jami’an sojin gwamnatin Kamaru da azabtar da mutane a yankuna da ake yin Magana da turancin Ingilishi a cikin kasar ta Kamaru.

A kan haka ta bukaci gwamnatinkamaru da kuma jagororin ‘yan awaren da su tabbatar da cewa sun dauki mataki na hana muzguna wa jama’a musamman fararen hula daga dukkanin bangarorin biyu, kuma su tabbatar da sun mika duk wanda aka samu da cin zarafin farar hula zuwa ga kotu domin hukunta shi.


Tags:
Comments(0)