​Macron Ya Gayyaci Haftar Zuwa Faransa Domin Tattaunawa

2020-02-13 19:07:44

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gayyaci madugun ‘yan hamayyar Libya masu dauke da makamai zuwa birnin Paris domin gudanar da wata tattaunawa.

Rahotanni daga kasar Libya sun sheda cewa, a ranar Laraba Haftar ya gana da babban jami’i a ma’aikatar harkokin wajen kasar Faransa mai kula da batun kasar Libya a birnin Benghazi na kasar ta Libya, inda ya mika wa Haftar wasikar Macron.

Wannan na zuwa ne bayan korafin da firayi ministan kasar ta Libya Faez Suraj ya yi ne, da ke cewa bangaren Haftar ba ya mutunta yarjejeniyar dakatar da bude wuta.

A ranar 19 ga watan Janairun da ya gabata ne dai aka gudanar da zaman tattaunawa kan batun rikicin kasar Libya a birnin Berlin na kasar Jamus, tare da halartar kasashen Amurka, Turkiya, Rasha, Italiya, Faransa, Birtaniya, da kanta Jamus mai masaukin baki, gami da bangarorin da ke rikici da juna a kasar ta Libya.

Kasashen Faransa da Masar, gami da Saudiyya da UAE ne suke mara baya ga Haftar, da nufin kwace iko da birnin Tripoli fadar mulkin kasar daga hannun gwamnatin Faez Suraj, wadda majalisar dinkin duniya ta amince da ita a hukumance.

Tags:
Comments(0)