​MDD: Ayyukan Kamfanoni Masu Gina Matsugunnan Yahudawa A Falastinu Ba Halastacce Ba Ne

2020-02-13 19:02:20

Majalisar dinkin dinkin dniya ta bayyana sunayen wasu kamfanoni masu aikin gina matsugunnan yahudawa a Falastinu da cewa aikinsu ba halastacce ba ne.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, majalisar dinkin duniya ta saka kamfanoni 112 da suke yi Isra’ila aikin gina matsugunnan yahudawa a cikin yankunan falastinawa a cikin kamfanonin da suka saba wa doka.

Daga cikin wadannan kamfanoni 112 da suke gina matsugunnan yahudawa a cikin yankunan falastinawa, 94 suna aiki ne kawai a cikin yankunan falastunawa da Isra’ila ta mamaye, yayin da 18 suna yin ayyuka a kasashe 6 na duniya.

Haka nan kuma bayanin ofishin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa, 95 daga cikin kamfanonin na Isra’ila ne, 6 kuam na Amurka, 4 na Holland, 3 na faransa, 2 na Burtaniya, 1 na Thailand, sai kuam wani 1 na Luxumburg.

Majalisar dinkin duniya da kungiyar tarayyar turai sun bayyana ayyukan mamayar yankunan falastinawa da Isra’ila take yi da cewa ya ya saba wa ka’ida, kuma matsugunnan yahudawan da ake ginawa a cikin wadannan yankuna ba su da halasci.

Tags:
Comments(0)