​Matakin Kasashen Turai Bisa Kan Da’awar Cewa Iran Ba Ta Mutunta Yarjejeniyar Nukiliya

2020-01-14 20:51:30

Manyan kasashen turai uku da suka rage a yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran a shekara 2015, sun kama hanyar daukar mataki kan ksar ta Iran, bisa da’awar cewa ta sabawa wasu bangarori na yarjejeniyar.

Kasashen da suka hada da Biritaniya, Jamus da kuma Faransa na zargin Iran da sabawa wasu dokoki da yarjejeniyar ta kunsa.

Matakin da kasashen turan ke son dauka zai iya kai su ga gabatar da batun a gaban kwamitin tsaro na MDD, domin neman kakaba wa Iran takunkumi bisa da’awar cewa ta sabawa wani bangare na yarjejeniyar, kamar yadda ta kunsa.

Kasashen turan dai na danganta matakin da na diflomatsiyya, maimakon kakaba wa Iran takunkumi.

A sanarwar bai daya da suka fitar ministocin harkokin wajen kasashen turan uku, Jean-Yves Le Drian, Dominic Raab da Heiko Maas, sun ce ba su da wani zabi illah bin wannan hanya don tankwaso Iran akan matakan da take dauka a baya bayan nan wanda suke cewa ya sabawa yarjejeniyar.

A ranar 5 ga watan Janairun nan ne, Iran ta sanar da daukan mataki na biyar na tatse sinadarin uranium dinta son rai, ba tare da kayyade shi kamar yadda yarjejeniyar ta tanada, a matsayin maida martaki kan ficewar Amurka daga cikin yarjejeniyar a shekara 2018, tare da sake kakaba mata jerin tsauraren takunkumai na karya tattalin arziki.

Tags:
Comments(0)