Faransa Ta Kara Fadada Karfin Sojinta A Yankin Sahel

2020-01-14 20:38:09

Kasashen kungiyar G5 Sahel, sun bukaci ci gaban kasancewar dakarun Faransa a yankin, a daidai lokacin da zanga zangar kyammar sojojin Faransar ke bazuwa a yankin.

Wannan bayyanin na kunshi ne a sanarwar bayan taron da shugaban kasar Faransa Emanuel Macron ya gudanar da takwarorin nasa na kungiyar ta G5 Sahel jiya Litini a birnin Pau.

Kasashen biyar da suka hada da (Chadi, Nijar, Mali, Mauritania da Burkina faso) tare da hadin guiwa da Faransa, sun sha alwashin yin aiki tare ta fuskar soji domin murkushe ayyukan ta’addanci.

Faransa ta bakin shugaba Macron, ta ce za ta aike da karin dakaru 220 a yankin na Sahel, bayan 4,500 da take dasu a yankin, domin karfafa wa ayyukan tawagarta ta Barkhane dake yaki da mayakan dake ikirari da sunan jihadi a yankin.

Shugaban na Faransa dai ya kirayi shuwagabannin na G5 sahel ne a taron na Pau, domin su fayyace masa matsayinsu akan makomar dakarun kasarsa a yankin.

Kasasshen Mali, Nijar Da Burkina Faso, sun jima suna fuskantar hare haren ta’addanci wadanda ke yin ajalin sojoji da fararen hula da da dama, na baya bayan shi ne wanda ya lashe rayukan sojojin Nijar 89 a yankin Shinagodar dake kusa da iyaka da Mali.

Wasu alkalumman da MDD ta fitar sun nuna cewa mutane 4,000 ne suka rasa rayukansu a kasashen Mali, da Nijar da Burkina a cikin shekara 2019 data gabata.

Tags:
Comments(0)