​An Tsawaita Tsagaita Wuta Da Kiran Taron Kasa da Kasa Kan Rikicin Libiya

2020-01-14 20:34:47

Rasha ta sanar da cewa shirin tsagita wuta na tsakanin bangarorin dake rikici a Libiya, zai ci gaba har sai abunda hali ya yi.

Wannan na zuwa ne bayan da Janar Khalifa Haftar dake rike gabashin Libiya ya fice daga kasar ta Rasha ba tare da sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta ba.

Mahukuntan na Rasha sun sanar da cewa Janar Haftar din ya bukaci karin kwanaki biyu domin yin nazari da kuma tuntubar sauren kabilu akan abunda yarjejeniyar ta kunsa.

A wani banagre kuma Kasar Jamus ta sanar cewa za ta karbi wani taron kasa da kasa kan rikicin Libiya a Ranar Lahadi mai zuwa.

Taron wanda za’a gudanar karkashin jagorancin MDD, zai yi kokarin hada hanyoyin cimma zaman lafiya a wannan kasa ta Libiya da rikici ya daidaita, kamar yadda gwamnatin kasar ta Jamus ta sanar yau Talata.

Saidai babu tabas akan ko jagororin bangarorin dake rikici a kasar ta Libiya zasu halarci taron.

Tags:
Comments(0)