Amurka Ta Kori Sojojin Saudiya 21 Da TaKe Bai Wa Horo, Bayan Harin Ta’addanci Na Jami’in sojan Saudiyya

2020-01-14 14:27:07

Amurka Ta Kori Sojojin Saudiya 21 Da TaKe Bai Wa Horo, Bayan Harin Ta’addanci Na Jami’in sojan Saudiyya.

Amurka ta bayyana cewa za ta tura sojojin Saudiyya 21 da take bai wa horo, zuwa gida bayan da bincike ya tababtar da cewa harin da wani jami’in sojan Saudiyya ya kai a kasar na ‘ta’addanci’ ne.

Babban mai shigar da kara na Amurka William Barr ya fada a ranar Litinin din da ta gabata cewa; Wanda ya yi harbin, ya tasirantu ne da tsattsauran ra’ayi.

Har ila yau William Barr ya ce an kori sojojin Saudiyya 21 da su ke karatun aikin soja a Amurkan, bayan binciken da aka gudanar akan wancan harin, kuma za a mayar da su gida.

Har ila yau, William Barr ya ce; Daliban sojan na Saudiyya suna hotunan da batsa da kananan yara a cikin wayoyinsu, haka nan kuma wasu bayanai masu alaka da tsattsauran ra’ayi.

A cikin watan Disamba na shekarar da ta gabata ne dai wani sojan Saudiyya Second Lieutenant Muhammad Saeed Alshamrani ya harbe sojojin Amurka uku tare da jikkawa wasu takwas a sansanin sojan Saman Amurka na Pensacola. Sai dai shi ma daga karshe wani dan sanda ya harbe shi har lahira.

Tags:
Comments(0)