Rahoto: Barnar Da Harin Iran Akan Sansanin Amurka A Iraki Ya Yi, Ya Dara Wanda Amurka Ta Bayyana

2020-01-14 13:34:34

A wani rahoto da dan rahoton tashar talabijin din kasar Denmark TV 2 ya shirya, wanda kuma a cikin ya yi hira da sojan kasar da ke zaune a sansanin soja na Ain al-Assad na Iraqi, da Iran ta kai wa harin daukar fansa, ya nuna cewa barnar da harin ya yi, ta dara wacce jami’an gwamnatin Amurka su ka bayyana.

Rahoton ya nuna sojan kasar Denmark Sergeant John tare da wasu sojojin kasar suna bayyana ra’ayoyinsu, bayan harin da Iran ta kai akan sansanin sojan Amurkan da yake a yankin Anbar.

“Ba zato ba tsammani ruwan makamai na farko ya zo, wannan shi ne abinda zan kira shi. Rokoki guda tara wadanda kowanensu ya kai ton guda su ka fara fadowa. Abu ne mai wuya a iya kwatanta shi. Ban taba shiga cikin wannan irin yanayin ba, kuma ina fata ba zan sake samun kaina a cikin yanayi irin wanna ba.” Abinda sojan kasar Denmark mai mukamin Sergeant ya bayyana kenan, wanda ya buya a cikin dakin karkashin kasa tare da sauran sojoji a lokacin da aka kai harin.

Ya kuma ci gaba da cewa; Harin farko ya yi muni ta yadda mun zaci cewa komai zai rushe babu abinda zai saura. Mun yi mamaki da rufin dakin da muke ciki bai rufto mana ba. Zan iya yin kiyasin cewa makamin roka mafi kusa da ya fado kusa da mu, bai wuce tazarar yadi 300 ba. Daga baya da muka fito muna zagayawa mun ga jirage masu saukar angulu sun dare gida biyu, ga kuma wasu manyan ramuka da za a iya shigar da babbar mota a ciki.

Tags:
Comments(0)