Zarif: Birtaniya Tana Yin Tarayya Da Amurka A Cikin Ayyukanta Na Ta’addancin Ba Tare Da Tunani Ba

2020-01-14 13:26:35

Minsitan harkokin wajen na Iran ya kuma yi kira ga kasashen turai da su cika alkawalin da ke wuyansu dangane da yarjejeniyar Nukiliya maimakon zama masu yin biyayya ga Amurka.

Da safiyar yau Talata ne dai ministan harkokin wajen na Iran ya wallafa a shafinsa na twitter cewa; Birtaniya tana maimaita abinda Amurkan take fada ne kamar tsuntsun Aku, kuma tana yin tarayya da ita a cikin dukkanin ayyyukan ta’addanci da take yi a cikin wannan yankin ba tare da tunani ba.

Ministan harkokin waje na Iran ya kuma cewa; Abin kunya na karshe wanda Birtaniya ta yi,shi ne biye wa Amurka da yi ma ta rakiya a yakar kasar Iraki. Sai dai abin tambaya anan shi ne me hakan ya jawo ma ta?

Tags:
Comments(0)