Madugun “Yan Tawayen Libya Ya Bar Kasar Rasha Ba Tare Da Ya Sa Hannu Akan Yarjejeniyar Tsagaita Wutar Yaki Ba

2020-01-14 13:22:19

An sami koma baya a kokarin da ake yi na tsagaita wutar yaki a kasar Libya, bayan da Halifa Hafitar ya fice daga kasar Rasha ba tare da ya rattaba hannu akan yarjejeniyar tsagaita wutar yaki ba.

Kasashen Rasha da Turkiya sun yi kokarin ganin an sami tsaiko a yakin da ake yi tsakanin gwamnatin Libya da ke Tripoli da kuma ‘yan tawayen da janar Halifa Haftar yake jagoranta.

Firai ministan kasar Libya Fayes al-Sarraj, da Halifa Haftar sun yi tattaunawa ta gaba da gaba ta tsawon sa’o’i, takwas bisa shiga tsakanin Mosocw da Ankara a babban birnin kasar Rasha a jiya Litinin.

Dazu ne dai ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bakin kakakinta Maria Zakharova ta sanar da cewa; Tare da cewa an kammala tsara sharuddan yarjejeniyar, sai dai Halifa Haftar ya fice daga kasar ba tare da ya rattaba hannu ba.

Sai dai duk da haka ministan harkokin wajen kasar ta Rasha Sergei Lavrov ya ce; Rasha za ta ci gaba da yin kokari domin ganin an kai ga cimma tsagaita wutar yaki.

Tags:
Comments(0)