​Shugaban Kasar Iran Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Maida Pentagon Hukumar Yan Ta’adda

2020-01-14 08:47:36

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya rattaba hannu kan dokar da majalisar dokokin kasar ta yi wa gyara, wacce kuma ta fadada dokar wacce aka samar da ita a cikin watan Afrilun shekarar da ta gabata, don ta game dukkan sojojin Amurka a duniya, a matsayin hukumar yan ta’adda.

Kafin haka dai gwamnatin Amurka da sanya IRGC a matsayin kungiyar yan ta’adda a shekarar da ta gabata, sai Iran kuma ta kafa dokar maida sojojin Amurka a yankin gabas ta tsakiya wato United States Central Command (CENTCOM) a matsayin yan ta’adda sannan bayan kisan Janar Sulaimani majalisar dokokin kasar ta fadada ta zuwa kan dukkan sojojin Amurka.

Tags:
Comments(0)