Kotu Ta Ba Wa Gwamnatin Nijeriya Ikon Kwace Gidajen Saraki Da Ke Ilorin

2019-12-02 19:45:26

Babbar kotun tarayya da ke Lagos ta ba wa hukumar EFCC mai fada da rashawa da cin hanci a Nijeriya ikon kwace wasu gidaje guda biyu da ke birnin Ilorin, fadar mulkin jihar Kwara mallakin tsohon shugaban majalisar tarayya ta kasar Bukola Saraki.

Alkalin kotun mai shari’a Rilwan Aikawa ne ya ba da wannan umurnin a cikin wani hukunci da ya yanke a yau din nan Litinin inda ya ba wa hukumar ta EFCC damar kwace wadannan gidaje guda biyu wadanda hukumar ta ce tsohon shugaban majalisar ya mallake su ne ta hanyar da ba ta dace ba.

Tun da fari dai hukumar ta EFCC ta ce bisa binciken da ta gudanar da kuma rahoton da kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa don sake dubi cikin shirin sayar da kayayyakin gwamnati da tsohuwar gwamnatin jihar Kwaran karkashin jagoran Bukola Sarakin ta gudanar daga shekara ta 2003 da 2011, an gano cewa lalle an tabka gagarumar almundahana, don haka ta bukaci kotun da ta ba ta damar kwace wasu kaddori na Dr. Bukola Sarakin wadanda ake ganin yana da hannu dumu dumu cikin wadannan almundahanan.

Wannan dai ba shi ne karon farko da hukumar ta EFCC take neman a ba da damar kwace kadarorin Dr. Sarakin ba a ci gaba da binciken da ake yi a kansa kan zargin da ake masa na watandar dukiyar jihar Kwaran a lokacin yana gwamnan jihar.

Tags:
Comments(0)