Iran: Za’a Biya Mutanen Da Aka Yi Wa Barna Yayin Rikicin Baya-Baya Na Iran

2019-12-02 19:42:03

Shugaban ma’aikatar shari’a kuma alkalin alkalai na kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewar lalle ya kamata a biya mutanen da aka cutar da su yayin rikicin baya-bayan nan da wasu kasashe suka haifar a kasar Iran.

Sayyid Ra’isi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron majalisar koli ta shari’a ta kasar Iran a yau Litinin inda ya ce barin mutane cikin wahalhalu wani lamari ne da ba za a taba yarda da shi ba, yana mai cewa mutane da aka cutar da su yayin rikicin suna da hakkin su bukaci a biya su barnar da aka yi musu.

Shugaban ma’aikatar shari’ar ya kara da cewa wajibi ne dukkanin hukumomi musamman gwamnati su tsaya kyam wajen ganin an biya mutanen da wannan rikici ya cutar diyyar irin barnar da aka yi musu ta rayuka ne ko kuma ta abin duniya.

Sayyid Ra’isi ya jaddada wa mutanen da rikicin ya cutar da cewa lalle ma’aikatar shari’a za ta tsaya da kuma taimaka musu wajen ganin an biya su hakkinsu.

Yayin wannan rikici da wasu suka kunna shi ta hanyar fakewa da batun karin farashin man fetur, an kona dukiyoyin gwamnati da na al’umma bugu da kari kan kashe wasu mutane da suka hada da jami’an tsaro da kuma fararen hula.

Tags:
Comments(0)