‘Yan Aware Sun Kai Hari Kan Wani Jirgin Fasinja A Kamaru

2019-12-02 19:36:31

Rikicin da ke tsakanin gwamnati da ‘yan aware na kasar Kamaru ya kara daukar wani sabon salo bayan harin da ‘yan awaren suka kai kan wani jirgin fasinja a lokacin da yake kokarin sauka a filin jirgin saman Bamenda da ke arewa masu yammacin kasar.

A wata sanarwa da Kamfanin jirgin sama na kasar Kamarun Cameroon Airlines ya fitar a yau din nan ya ce jirgin dai ya taso ne daga birnin Doula amma kuma ya sauka lafiya ba tare da wani fasinja ya sami rauni ba duk kuwa da harin da aka kai masan.

Su dai ‘yan awaren ta bakin daya daga cikin jagororinsu kuma shugaban majalisar Ambazonia ta ‘yan awaren, Cho Ayaba, yace gwamnati tana amfani da jiragen fasinjan ne wajen jigilar sojoji da makamai, kuma tuni suka ja kunnen kamfanin da kuma fasinjojinsa cewa lalle za a harbo duk wani jirgin da ya tashi ba tare da an gabatar musu da bayanai kansa cikin lokaci ba.

Tun a shekara ta 2017 ne yankin masu magana da harshen turancin Ingila na kasar Kamarun ya zamanto wani filin daga tsakanin sojojin gwamnati da na ‘yan awaren lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa daga bangarori biyun.

Tags:
Comments(0)