Gwamnatin Mali Ta Sanar Da Ranar Fara Tattaunawar Kasa Don Magance Rikicin Kasar

2019-12-02 19:32:19

Gwamnatin kasar Mali ta sanar da ranar 14 ga watan Disamban nan da muke ciki a matsayin ranar da za a fara taron tattaunawa ta kasar da nufin kawo karshen rikicin siyasar da ya ki ci ya ki cinyewa a kasar.

Shugaban kasar Malin Ibrahim Keita ne ya sanar da hakan inda ya ce manufar taron dai ita ce tattaro ‘yan kasar kan teburin tattaunawa a tsakaninsu da nufin shata wata taswiwar hanya da za ta ceto kasar daga rikicin siyasar da take fuskanta, yana mai cewa an tsayar da ranar da ne bayan tattaunawa da bangarori daban-daban na masu ruwa da tsaki na kasar.

Wasu kungiyoyin ‘yan adawa na kasar dai sun bayyana dari-darinsu dangane da taron suna masu cewa ba ma za su halarci taron ba; lamarin da ake ganinsa a matsayin wani abin da zai iya kawo cikas ga wannan kokari na zaman lafiya a kasar.

Tun a shekara ta 2012 ne dai kasar Malin ta fada cikin rikice-rikice na siyasa lamarin da ya share fagen kungiyoyin ‘yan ta’adda kame yankuna da dama na kasar.

Kasashen duniya musamman kasar Faransa dai ta tura sojojinta kasar Malin da nufin fada da ‘yan kungiyoyin ta’addancin sai dai kuma har ya zuwa yanzu da dama daga cikin ‘yan kasar suna ci gaba da sukar kasar Faransan wadanda suke ganin tana da hannu cikin wannan rikicin, kana kuma babu abin da ta fi ba shi muhimmanci in ba kare manufofin, ba tare da damuwa da manufofin al’ummomin Mali din ba.

Tags:
Comments(0)