Iran A Shirye Ta Ke Ta Warware Sabanin Da Ke Tsakaninta Da Amurka

2019-12-02 15:00:54

Shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Ali Larijani ya bayyana cewa; A kodayaushe Iran tana cikin shiri domin ta warware matsalar da ta ke tsakaninta da Amurka.

Shugaban Majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya bayyana haka ne a yayin da ya ke gabatar da taron manema labaru a nan birnin Tehran, a jiya Lahadi.

Larijani ya kara da cewa; Ya kamata Amurka ta fahimci cewa siyasarta ta matsin lamba mai tsanani ta ci kasa, don haka ya kamata ta yi watsi da ita.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa akan abubuwan da su ka faru a kasar Iraki, shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kara da cewa; Iran ba ta da wata damuwa saboda akwai Ayatullah Ali Sistani wanda nasihohinsa za su warware matsalar da kasar take fama da ita.

A jiya Lahadi ne dai majalisar dokokin kasar Iraqi ta sanar da amincewa da takardar sauka daga aiki da Fira minister Adil Abdul Mahadi ya aike mata. Matakin na Fira minista ya biyo bayan kiran da Ayatullah Sayyid Ali Sistani ga majalisa da ta dauki matakin kawo karshen rikicin kasar.

Tags:
Comments(0)