Araqhchi Yana Ziyarar Aiki A Kasar Japan

2019-12-02 14:55:30

Mataimakin ministan harkokin wajen Ira Abbas Araghchi ya isa birnin Tokyo a ranar Litinin domin bude tattaunawa da jami’an kasar domin alakar da ke tsakaninsu.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya shaida wa kafanin dillancin labarun “Irna” cewa; Har yanzu kasashen turai suna daukar batun kafa asusun musayar kudade na “ INSTEX’ da muhimmanci domin suna yi masa ganin hanyar da mu’amala ta kudade tsakaninsu da Iran.

Tun da fari kasashen Belgium, Danmark,Sweden, Finland, Norway da kuma Netherlands sun fitar da sanarwa akan shigar su cikin shirin Asusun na “ Instex” domin yin huldar kasuwanci da Iran, da kuma ganin an tseratar da yarjejeniyar Nukiliya daga durkushewa.

An kafa asusun na “INSTEX” ne domin kaucewa takunkuman da Amurka ta kakabawa Iran da hana cutar da kamfanonin kasashen turai da su ke son yin cinikayya da Iran

Tags:
Comments(0)