Mutane 378 Ne Suka Yi Rijistar Tsayawa Takara A Majalisar Iran

2019-12-02 10:00:01

Ministan harkokin cikin gidan kasar iran Abdurrida Rahmani a lokacin da yake ganawa da manema labaria ya bayyana cewa daga lokacin fara rijistar sunayen masu san tsayawa takarar majalisar shawarar musulunci ta kasar, kimain mutane 378 ne suka rubuta sunayensu, kuma ana fatan gudanar da zaben yan majalisun cike da tsafta tare da kiyaye dokoki.

Kana ya jaddada game da muhimmancin ci gaba da tuntubar juna tsakanin majalisar fayyace maslahar tsarin mulki da sauran bangarorin da abin ya shafa , ya zuwa yanzu an bude runfunan rijistr sunayen yan takara guda 208 a fadin kasar,

Za’a gudanar da zaben majalisar shawarar musulunci ne a ranar 21 ga watan fabareru mai kamawa.


Tags:
Comments(0)