Mutane 14 Sun Rasu A Harin Da Aka Kai A Wata Majami’a A Borkina Faso

2019-12-02 09:36:25

Tashar talbijin din Rasha Today ta nakalto cewa wasu mutane da ba’a san ko su waye ba sun kai hari kan wata Majami’ar kiristoci yan darikar Prostostant a garin Hantokoro da ke gabashin kasar Borkina Faso da ke kusa da iyakarta da kasar Niger, kuma yayi sanadiyar rasa rayukan masu ibada guda 14.

Kafafen watsa labarai a kasar ta Birkina Faso su bayyana cewa an kai harin ne a lokacin da ake gudanar da bukin Adduo’i inda wasu mutane da ba’a san ko su waye ba suka kai hari da yayi sanadiyar mutuwar masu Ibada tsakanin 10 zuwa 14, sai dai har yanzu kafafen watsa labarai na hukuma ba su ce uffan game da harin ba,

Har yanzu babu wata kungiya da ta sanar da alhakin kai harin, idan ana iya tunawa kasarts Borkina na fuskantar hare hare yan ta’adda, da a wasu lokutan ake amafanin da su wajen haifar da rikicin addinin tsakanin mabiya addinai a kasar dama wasu kasashen Afrikadomin cimma manufofin siyasa.

Tags:
Comments(0)